Daukaka Ga Allah by Abel Obaje — Lyrics

Abel Obaje Hausa Gloria Solfa notation

Full Lyrics

CHORUS Daukaka ga Allah a cikin Samaniya VERSE 1 A duniya kuma salama ga mutane na kwarai mai kyau Muna yabonka Muna albarkatenka Muna yi maka sujada Muna daukakanka Muna yi maka sujada saboda darajarka Godiya saboda darajarka mai girma VERSE 2 Ya Ubangiji Allah Sarkin Sama Allah Uba Mai Iko duka Ya Ubangiji Yesu Almasihu da makadaici Ya Ubangiji Allah dan tunkiya na Allah Dan tunkiya na Allah, Dan Uba VERSE 3 Kaida ke kawar da zunuban duniya, kayi mana jinkai Kaida ke kawar da zunuban duniya, kaji addu'ar mu Kaida kake zaune a hannun dama na Uba, kayi mana jinkai VERSE 4 Domin kai kadai mai tsarki ne Kai kadai madaukaki ne Kai kadai madaukaki ne, Ya Yesu Almasihu Tare da Ruhu Mai Tsarki, cikin darajan Allah Uba Amin, Amin, Amin

Download the sheet music

Daukaka Ga Allah

Daukaka Ga Allah

By Abel Obaje
Solfa
Hausa
2 pages
61 Downloads
Gloria
0 0

More lyrics you may want