Full Lyrics
CHORUS
Daukaka ga Allah a cikin samaniya,
Daukaka ga Allah a cikin samaniya.
VERSE 1
A duniya kuma salama ga mutane na nufi mai kyau,
Muna yabonka, muna albarkatarka,
Muna sujada, muna daukakanka,
Muna yimaka sujada saboda darajarka mai girma,
Godiya saboda darajarka mai girma.
VERSE 2
Ya ubangiji Allah, Sarkin sama,
Allah uba mai iko duka,
Ya ubangiji Yesu Almasihu dan makadaici,
Ubangiji Allah, dan tunkiya na Allah, dan uba.
VERSE 3
Kai da ke kawar da zunuban duniya, kayi mana jinkai,
Kai da kake kawar da zunuban duniya, kaji addu'armu,
Kai da kake zaune a hannun dama na uba, kayi mana jinkai.
VERSE 4
Domin kai kadai mai tsarki ne,
Kai kadai ubangiji ne,
Kai kadai mai daukaka ne, ya Yesu Almasihu,
Tare da Ruhu Mai Tsarki cikin darajar Allah uba.
Amin, Amin, Amin.