Full Lyrics
[HAUSA VERSION]
[REFRAIN]
Dukan Al'umma za su durkusa a gabanka su bauta maka, ya Ubangiji.
[VERSE 1]
Ka koya wa Sarki ya yi shari'a da adalcin ka ya Allah.
Ka kuma bashi shari'ar ka don ya yi mulkin jama'ar ka,
Don ya yi mulkin jama'ar ka bisa kan shari'ar ka ya kuma bi
da adalci kasa Sarki ya yi wata laka wa shari'ar gaskiya.
[VERSE 2]
Ka sa adalci ya bunkasa a zamanin sa wadata ta dawama
muddin wata na haskaka wa mulkin sa ya kai daga teku zuwa teku.
Daga Kogin Yufiretis har zuwa iyakar duniya.
[VERSE 3]
Sarakunan Esbanya da na Tsibirai, zasu bashi kyautai.
Sarakuna Arabiya da na Habasha zasu kawo masa kyautai,
Dukan Sarakuna zasu durkusa a gaban sa dukan sauran
Al'umma zasu bauta massa!
[VERSE 4]
Yakan ceci matalauta wadanda suka yi kira gareshi.
Da wadanda suke da bukata da wadanda ba su kula da su.
Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta.
Yakan ceci rayukan wadanda ke da bukata.
[ENGLISH VERSION]
[REFRAIN]
All nations shall fall prostrate before you, O Lord.
[VERSE 1]
O God give your judgement to the King to a king's son your justice,
That he may judge your people in justice, and your poor in right judgement.
[VERSE 2]
In his days shall justice flourish and great peace till the moon is no more.
He shall rule from sea to sea from the river to the bounds of the earth.
[VERSE 3]
The Kings of Tarshish and the Islands shall pay tribute.
The Kings of Sheba and Sheba shall bring him gifts.
Before him all Kings shall fall prostrate all nations shall serve him.
[VERSE 4]
For he shall save the needy when they cry the poor and those who are helpless
He will have Pity on the weak and the needy, and save the lives of the needy.