Full Lyrics
CHORUS
Ku ci jikinsa, ku sha jininsa abinci ne kyauta
Shi ya ba mu da kansa domin mu sami ceto namu
Sabuwar alkawari ta sabuwar ceto ta
Sabuwar hanya
VERSE 1
Abinci ne mai dadi
abinci ne mai kyau
abincin ceto wanda Shi Yesu ya
bawa duniya
don watan wata rana mu ma
mu nuna wa 'yan'uwa
VERSE 2
Idan mun ci burodi
mun sha calis na wain
jiki da jini wanda Shi Yesu ya
bawa duniya
don watan wata rana mu ma
mu nuna wa 'yan'uwa
VERSE 3
Mu sa ido ga Yesu
wanda Uba ya aiko
domin mu sami wannan salama ta
bawa duniya
don watan wata rana mu ma
mu nuna wa 'yan'uwa
VERSE 4
Idan mun ga kasawa
idan fa muna yunwa
ga abincin ruhu da Shi Yesu ya
bawa duniya
don watan wata rana mu ma
mu nuna wa 'yan'uwa
VERSE 5
Ku zo wurin Dan Allah
Ku zo wurin mai rai
ga Dan tunkiya wanda Shi Allah ya
bawa duniya
don watan wata rana mu ma
mu nuna wa 'yan'uwa