Full Lyrics
VERSE 1
Yesu kiristy zaya zo cikin wannan duniya,
domin ya sharanta wannan duniya,
shi da kansa zaya zo cikin wannan duniya,
zaya nuna Ikonsa a randa zai zo;
REFRAIN
Duk abinda zaka yi a wannan rayuwa
kasancewa akwai randa zaka bar duniya,
ko in Yesu bai zoba mutuwa zaya zo,
belle ma Yesu zai zo domin yin shari'a.
VERSE 2
Mai yin adalci kaci gaba da adalcin ka,
mai yin mugunta kuma cigaba da yi,
komai da lokacinta agogo na yin aikin sa,
sai kayi tunani akan rayuwan ka;
VERSE 3
Cikin farkon halitan duniya akwai kalma,
Kalmar kuma na tare da Allah Uba,
Kalman nan bishara ce zuwa a gare mu,
zai zo ya sharanta wadanda suka ji;
VERSE 4
Manzane sun rubuta zuwan dan ragon Allah,
Fristoci sun bayyana yanda zaya zo,
cikin gajimare ne dan ragon Allah zai zo,
tare da malaikun sa domin yi shari'a.