Daukaka ga Allah by Dauda D. Zih — Lyrics

Dauda D. Zih Hausa Gloria Mass Settings Solfa notation

Full Lyrics

CHORUS Daukaka ga Allah Cikin Samaniya, Daukaka ga Allah Cikin Samaniya. Oh, Daukaka ga Allah, Allah Cikin Samaniya, Oh, Daukaka ga Allah a cikin Samaniya. VERSE 1 A duniya salama ga mutane na nufi mai kyau, Mu na yabon ka mu na albarkace ka. Mu na yi ma ka sujada, mu na daukaka ka, Mu na yi maka godiya saboda darajar ka mai girma. Ya Ubangiji Allah Sarkin sama, Allah Uba mai iko duka. Oh! VERSE 2 Ya Ubangiji Yesu Kristi da makadaici, Ubangiji Allah dan tunkiya na Allah. Ya Ubangiji Allah, dan Uba, Kai da ka kawar da zunuban duniya Ka yi ma na jinkai, ka yi ma na jin kai, Kai da ka kawar da zunuban duniya. Oh! VERSE 3 Ka ji addu'ar mu, ka ji addu'ar mu, Kai da ka ke zaune a hanun dama na Uba. Kayi mana jinkai, ka yi ma na jinkai, domin kai Kadai mai tsarki ne. Kai kadai Ubangiji ne, Kai kadai Madaukaki ne. Ya Yesu, ya Yesu Kristi, tare da Ruhu mai tsarki. Cikin darajar Allah Uba Amin.

Download the sheet music

Daukaka ga Allah

Daukaka ga Allah

By Dauda D. Zih
Solfa
Hausa
3 pages
2 Downloads
Gloria Mass Settings
0 0

More lyrics you may want