Full Lyrics
VERSE 1
Yesu ya yi addu'a, a Jathsaimani,
Jibin sa, ya zama jini suna faduwa.
Malaikan Ubangiji danga chan sama,
ya sauko ya zo wurin sa ya karfa shi.
VERSE 2
Yesu ya zo ya iske, Almajiran sa,
Dukan su, sun kasa tsaro ko sa'a daya.
Ruhu ya yarda amma jiki raunana,
yana ke tafiya ta biyu ya yi addu'a.
VERSE 3
Ya zo ya sake iske, Almajiran sa,
Sun kasa, su yi addu'a suna barci.
Sai ya tafi ta uku ya yi addu'a,
ya dawo lokaci ya yi za a bashe shi.
REFRAIN
A Jathsaimani, a Jathsaimani,
chan Yesu ya ce;
"Ya Uba! Ina rokon ka
idan ka yarda.
Ka kawas mini, dauki wannan koko.
Amma dai ba nawa nufi naka za a yi."
PRAYER
"Ya Ubangiji Allah, kada ka bar mu da tunanin kanmu, amma bari nufin ka ya cika. Amin."